Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Indiya da Pakistan sun yi Musanyar Wuta - 2002-01-20


Sojojin Pakistan da na Indiya sun yi musanyar wuta da kananan bindigogi yau lahadi a bakin iyakar da suke rikici kai a cikin yankin Kashmir. Irin wannan musanyar wuta ta zamo ruwan dare cikin ’yan makonnin nan, tun lokacin da aka girka dubban sojoji a bakin iyakar a bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai kan majalisar dokokin Indiya, a birnin New Delhi, a watan jiya.

Indiya ta dora laifin wannan hari a kan masu kishin addini dake Pakistan, ta kuma bukaci hukumomi a birnin Islamabad da su dauki matakan kai tsaye na hana kai hare-haren ta’addanci daga tsallaken iyaka.

XS
SM
MD
LG