Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha na Binciken Kashe Sojojinta da aka yi a Dagestan - 2002-01-20


Hukumomin Rasha suna binciken tashin wani bam wanda ya kashe sojoji bakwai ya raunata wasu guda uku a jamhuriyar Dagestan dake kudancin kasar. Rahotanni daga Makachkala, babban birnin jamhuriyar, sun ce bam da aka cika shi da kusoshi da karafa, wanda kuma ake danawa ko tayarwa da na’ura daga nesa, watau “Remote Control”, ya tashi a tsakiyar birnin, dab da wata motar soja dake dauke da mutane 30. Sojoji biyar sun mutu nan take, biyu kuma suka cika a asibiti. Jami’an Rasha da ’yan sandan jamhuriyar sun dora laifin wannan hari na ranar Jumma’a a kan ’yan tawaye daga makwabciyarsu Chechnya, suna bayyana harin a zaman na ta’addanci.

Kamfanonin dillancin labarai na Rasha sun ambaci wasu jami’an Dagestan suna fadin cewa watakila su ma ’yan tawayen jamhuriyar suna da hannu a wannan harin.

XS
SM
MD
LG