Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yasser Arafat Ya Ce Yana Yakar Ta'addanci - 2002-01-20


Shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, ya ce yana yin bakin kokarinsa domin hana kai hare-haren ta’addanci kan Isra’ila, musamman ma na kunar bakin wake. A cikin hirar da yayi da mujallar Newsweek, Malam Arafat yayi zargin cewa firayim minista Ariel Sharon na Isra’ila yana fakewa ne da batun ta’addanci domin ya wargaza shirin wanzar da zaman lafiya.

Malam Arafat ya ce hukumar mulkin kai ta Falasdinu ta kama mutane fiye da 250 a kokarin da take yi na murkushe kungiyoyin ta’addanci a yankin yammacin kogin Jordan da zirin Gaza.

Shugaban na Falasdinawa ya bayyana mamakin yadda kasashen duniya suka yi ko oho da take-taken Bani Isra’ila kamar kawanyar wata guda wadda ta hana masa fita daga hedkwatarsa a garin Ramallah dake yankin yammacin kogin Jordan.

XS
SM
MD
LG