Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin China da Amurka Sun yi Gum da bakinsu - 2002-01-20


Jami’ai a Beijing da nan Washington sun ki cewa uffan game da rahotannin da aka wallafa cewar China ta gano na’urorin satar jin maganganu boye cikin wani jirgin saman da aka kerawa shugaba Jiang Zemin a nan Amurka.

A jiya asabar jaridar "Financial Times" ta London ta buga labarin cewa jami’an leken asirin China sun gano na’urorin zamani fiye da 20 masu kaifin gaske na satar jin maganganu boye a cikin wannan jirgi samfurin Boeing 767. Ita ma jaridar "Washington Post" ta buga labari jiya asabar cewa jami’an gwamnatin China suna zargin hukumomin leken asirin Amurka da laifin dasa wadannan na’urori.

Amma kuma a yau lahadi jami’an gwamnatin China sun shaidawa kamfanonin dillancin labaran kasashen yammaci cewar babu wani wanda zai yi sharhi kan wannan batu. Fadar White House da ma’aikatar harkokin wajen Amurka su ma sun ki su gaskata ko kuma su musanta wannan rahoto.

XS
SM
MD
LG