Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Tsagaita Wutan Sudan zai soma aiki yau - 2002-01-22


Wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin Sudan da kuma ‘yan tawaye wadda zata kawo karshen yake yaken da suke a yankunan tsakiyar kasar, zata soma aiki daga yau dinnan (Talata). An samar da yarjejeniyar ne da nufin kyale kayayyakin agajin ceton rai su isa ga yankunan tsaunukan Nubia. Gwamnatin Sudan a Khartoum tareda kungiyar ‘yan tawayen Kudancin kasar ta SPLA suka cimma yarjejeniyar a tattaunawar da suka gudanar a kasar Switzerland a ran Asabar. Karkashin shirin, ana iya sake sabunta yarjejeniyar a kowadanne watanni shida-shida. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya bada rahoto dake cewa sojin Sudan sun rigaya sun karbi umurni dake cewa lallai su soma amfani da yarjejeniyar daga karfe tara agogon UTC (takwas agogon Najeriya) a yau. Karkashin amincewar da aka cimma wadda Amirka da Switzerland suka taimaka hadawa, bangarorin biyu sun kuma amincewa kyale masu kula daga wasu kasashen waje su zuba ido suna kula da shirin na tsagaita wuta.

XS
SM
MD
LG