Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Tsohon Madugun Kiristoci a Beirut - 2002-01-24


An kashe wani tsohon Minista kuma kwamandan kiristoci mayakan sa kai a Lebanon, Mr. Elie Hobeika, a sanadiyyar fashewar bam cikin wata karamar mota a kusa da gidansa dake birnin Beirut. ’Yan-sandan Lebanon sun ce an kuma kashe uku daga cikin masu gadin Mr. Hobeika, da kuma wani mutumin, a wannan bam da ya yi bindiga a unguwar Hazmieh ta yankin gabashin birnin na Beirut.

‘Yan-sandan sun ce, nakiyar ta yi bindiga ne, a daidai lokacin da Mr. Hobeika yake shirin shiga wata motarsa ta soja mai sulke. Nan take, babu wanda ya dauki alhakin kai wannan farmaki. Mr. Hobeika shi ne tsohon jagoran mayakan sakan rundunar kiristoci dakaru a Lebanon mai samun goyon bayan Isra'ila, kungiyar da ta kashe daruruwan Palasdinawa a sansanonin ‘yan gudun hijira na Sabra da Shatila, a lokacin da Isra'ila ta mamaye Lebanon, cikin shekarar dubu da dari tara da tamanin da biyu (1982).

XS
SM
MD
LG