Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sakataren MDD Zai Gana da Shugaba Musharraf - 2002-01-24


Babban magakatardar Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, zai gana da shugaba Pervez Musharraf na kasar Pakistan wani lokaci a yau Alhamis, inda zasu tattauna batun hanyar da za‘a kai ga saukaka zaman tankiyar da ake yi tsakanin Pakistan da Indiya. Ana kuma kyautata cewar tattaunawar zata taimaka wajen bada goyon baya da karfafa gwiwar gwamnatin wucin gadin Afghanistan.

Zaman tankiya tsakanin Indiya da Pakistan ya kara zafafa a bayan wasu hare-haren da ’yan ta‘adda suka kaiwa ginin majalisar dokokin Indiya a watan da ya gabata, sannan aka sake samun wani harin da wani dan bindigar ya kaiwa cibiyar al‘adu ta Amurka dake birnin Calcutta.

Pakistan ta musanta cewa tana da hannu wajen shirya kai hare-haren.

Bayan an kammala wannan tattaunawar a Islamabad, sakatare Annan zai wuce zuwa Afghanistan, inda zai tattauna tare da shugaban gwamnatin wucin gadi, Hamid Karzai. Babban magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya zai kuma kai ziyarar aiki kasar Iran wadda ke makwabtaka da Afghanistan.

XS
SM
MD
LG