Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Agaji a Kwango Kinshasa Zasu Fara Rarraba Tabarmin Roba - 2002-01-24


Ma’aikatan agaji a Jamhuriyar Dimokradiyya ta Kwango, watau Kwango Kinshasa, suna can suna haramar fara rarraba wasu irin tabarmi na roba da barguna a birnin nan na Goma, inda aman wutar da wani dutse ya yi cikin makon jiya, ta sa dubun dubatar jama’a suka rasa gidajensu. Yayinda a yau alhamis aka cigaba da rarraba irin wadannan kayayyaki, ana nan kuma ana jigilar jarekanin ruwa, da yanar hana shakar kura mai guba, da kuma tanfal daga masu bada agaji daban-daban.

Yanzu haka dai, an tabbatar da cewa ruwan sha a wannan yanki yana da kyau, duk da fargabar da aka yi da farko, cewa, mai yiwuwa tokar dutsen ta haddasa guba a cikin ruwan.

Ta daya gefe kuma, ma’aikatan agajin suna tararrabi cewa, watakila, za a cigaba da samun afkuwar girgizar kasa jefi-jefi, mai nasaba da aman da dutsen ya yi. Jakadan Kwango Kinshasa a Majalisar Dinkin Duniya, Antonie Mindua ya yi kira ga kasashen duniya da su agazawa kasarsa da kudi dala miliyan goma.

XS
SM
MD
LG