Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Ba'Amurke Dan Taliban A Kotu - 2002-01-24


An tuhumi John Walker Lindh, Ba'Ameriken nan wanda ya yiwa kungiyar Taleban yaki, da laifin kulla makarkashiyar kashe Amerikawa dake kasashen waje tare da taimakon wata kungiyar ’yan ta’ada. An dauki tsauraran matakan tsaro sosai a lokacin da ya isa wata kotun dake wajen birnin Washington a yau alhamis.

A lokacin da alkali ya tambaye shi ko ya fahimci irin zarge zargen da ake yi masa da kuma irin hukuncin da za’a iya yanke masa, sai Mr. Walker wanda yayi aski yace ya fahimci haka. In dai har aka sami Mr. Walker, dan shekara ashirin da haihuwa, da laifi, ana iya yanke masa hukumcin daurin rai da rai.

Yanzu dai za a ci gaba da tsare shi ba tare da beli ba har nan da makonni biyu, lokacin da za’a fara yi masa shari’ar. Bayan wannan zama, mahaifin Mr. Walker ya fada wa ’yan jarida cewa dansa ba shi da laifi kuma bai taba niyyar raunata Amerikawa ba.

XS
SM
MD
LG