Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bayyana Sunayen Wakilan Hukumar Afghanistan - 2002-01-25


Majalisar Dinkin Duniya, ta fadi sunayen wakilai 21 na hukumar Afganistan, wadda za ta kafa babbar majalisar gamin-gambiza ta dukkan kabilun kasar da akafi sani da suna, majalisar Loya-Jirga, domin ta aza harsashen matakan da za a bi wajen kafa wata zababbiyar gwamnati nan gaba.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Afganistan din, Hamid Karzai, shi ne ya baiyana sunayen ‘yan majalisar, a wani taron hira da manema labarai na hadin gwiwa da suka yi da babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, wanda ya kai ziyara kasar.

Mr. Annan ya yi amanna cewa, sabanin da aka samu a tsakanin bangarorin Afghanistan daban-daban, shi ne ya janyo jinkirin kafa wannan majalisa, yana mai yin kira ga dukkan al’ummar kasar su yi aikin kafa irin wannan majalisa ta gamin-gambiza. Tuni dai, bangarorin na Afghanistan suka amince, wannan majalisa, ta zabi wakilan wata gwamnatin wucin gadin, wadda za ta yi aikin watanni 18, bayan cikar wa’adin wadda ake da ita yanzu na tsawon watanni shida.

XS
SM
MD
LG