Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Madagascar Ta Yanke Hukumci Kan Zabe - 2002-01-25


Kotun kolin kasar Madagascar ta tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin watan jiya, tana mai bada umarnin a fafata zabe zagaye na biyu, saboda babu dan takarar da ya samu cikakken rinjaye da ake da bukata.

Rahotanni daga Antananarivo, babban birnin Madagaskar, sun ce, cikin kwana talatin nan gaba, za a yi zaben turmi na biyu, inda shugaba mai ci-yanzu Didier Ratsiraka, zai fafata da babban mai hamaiya da shi, Marc Ravalomanana, Magajin garin, babban birnin kasar.

Kotun kolin ta ce, shugaba Ratsiraka ya samu kashi 41 cikin dari na kuri’un da aka kada cikin watan jiya, shi kuma mai hamaiya da shi, ya tashi da kashi 46 cikin darin. Dubun dubatar jama’a sun shafe makwanni suna zanga-zangar nuna goyon baya ga Mr. Ravalomanana, wanda yake ikirarin cewa, ya samu fiye da kashi hamsin cikin dari, a kuri’un da aka jefa ranar 16 ga watan jiya (disamba)

XS
SM
MD
LG