Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Turai Zata Guji Sanyawa Zimbabwe Takunkumi - 2002-01-25


Ma’aikatan diflomasiyya sun ce da alamun Kungiyar Tarayyar Turai ba zata kakaba wa Zimbabwe takunkumi a taron ministocin harkokin wajenta da za a yi ranar litinin a Brussels ba.

Jami’an diflomasiyyar kasashen turai sun ce kakaba takunkumi a daidai wannan lokacin zai biya muradun shugaba Robert Mugabe, ya kuma zamo hujjar da zai rabe da ita wajen kara kuntatawa ’yan adawa.

Ma’aikatan diflomasiyyar suka ce suna son ganin yadda lamarin zai kasance kafin zaben shugaban kasa na watan Maris, inda shugaba Mugabe yake fuskantar hamayya mai zafi daga madugun ’yan adawa, Morgan Tsvangirai. Har ila yau shugaba Mugabe yana fuskantar suka mai kara zafi daga kasashen waje kan yadda gwamnatinsa take danne ’yan jarida da ’yan adawa.

XS
SM
MD
LG