Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Falasdinawa Tayi Kiran A Daina Kai Hare-Hare - 2002-01-26


Majalisar mulkin kai ta Falasdinawa tayi kira ga ’yan kishin Falasdinu da su daina kai hare-hare kan Isra’ila. Shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, ya gana da ’yan majalisar zartaswarsa har zuwa cikin daren jiya Jumma’a, daga bisani suka bada sanarwar dake kira ga dukkan bangarorin su yi aiki da shirin tsagaita wuta, suna masu fadin cewa hare-haren da ake kaiwa kan Isra’ila suna tauye muradun Falasdinawa.

Wannan roko ya zo a bayan da jami’an Amurka suka gana domin nazarin irin matakan da zasu dauka a kan Malam Arafat, bayan da suka tantance cewar majalisar mulkin kai ta Falasdinawa tana da hannu a yunkurin da ya ci tura na yin fasa kwabrin makamai makare da wani jirgin ruwa zuwa cikin Gaza.

A can gefe guda kuma, jiragen saman yaki na isra’ila sun kai hare-hare kan cibiyoyin Falasdinawa a wani bangaren martanin harin bam na kunar bakin wake da ya raunata ’yan Isra’ila 26 a birnin Tel Aviv.

XS
SM
MD
LG