Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Majalisar Dokoki Sun Ce Ana Kulawa Sosai da Fursunoni - 2002-01-26


Wasu 'yan majalisar dokokin Amurka sun ce ana kulawa sosai da mayakan al-Qa’ida da na Taleban da ake tsare da su a sansanin mayakan ruwan Amurka dake Guantanamo Bay a tsibirin Cuba. A jiya Jumma’a ‘yan majalisar dokoki su kimanin 20 sun yi rangadin wannan sansani da ake kira Camp X-Ray, inda Amurka take tsare da fursunoni 158 da ta kamo daga Afghanistan. Bakin dukkan ’yan majalisar ya zo daya kan cewa ana kula da wadannan fursunoni.

Wasu kungiyoyin kare hakkin Bil Adama na kasa da kasa sun yi Allah wadarai da halin da mutanen suke ciki a wannan sansani, a bayan da aka nuna hotunan fursunonin suna durkushe an daure hannaye da kafafuwansu da sarka, an rufe musu idanu da kyalle aka kuma toshe musu kunnuwa.

A gobe lahadi sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, zai ziyarci sansanin.

XS
SM
MD
LG