Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Nemi Karin Kudin Tsaron Cikin Gida - 2002-01-26


Shugaba Bush ya ce zai nemi majalisar dokoki ta ba shi karin kudi domin kare Amurka daga hare-haren ta’addanci. Mr Bush ya ce a wajen gabatar da jawabinsa na halin da kasa take ciki ranar talata a gaban majalisa, zai nemi da a ninka masa yawan kudin da aka kasafta domin tsaron cikin gida zuwa dala miliyan dubu 38. Ya ce tsaron cikin gida shine batu mafi muhimmanci a wurinsa, yana mai cewa za a yi amfani da dala miliyan dubu 11 domin kare Amurka daga kowane irin hari, ta sama ko ta kasa ko daga teku.

A can wani gefen kuwa, babban kwamandan sojojin Amurka a Afghanistan, Janar Tommy Franks, ya ce wani batun da Amurka ta dorawa muhimmanci shine hana kai sabbin hare-haren ta’addanci a fadin duniya. A lokacin da yake magana a Islamabad, babban birnin Pakistan, Janar Franks ya kara da cewa sojojin Amurka suna ci gaba da farautar Osama bin Laden, shugaban kungiyar ’yan ta’adda ta al-Qa’ida, da kuma hambararren shugaban ’yan Taleban, Mullah Mohammad Omar.

Janar Franks yayi magana a bayan da ya kammala wata gajeruwar ziyara jiya Jumma’a a Kabul, babban birnin Afghanistan, inda ya tattauna batutuwan tsaro da manyan jami’an gwamnatin rikon kwarya. A yau asabar shugaban gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan Hamid Karzai, zai taso zuwa nan Amurka, inda zai gana da shugaba Bush da manyan jami’ai.

XS
SM
MD
LG