Indiya tayi bukin ranar Jamhuriya, inda aka dauki tsauraran matakan tsaro, aka kuma rage tsawon faretin sojoji, yayin da aka girka dubun dubatan sojoji a bakin iyakarsu da Pakistan inda ake tankiya.
Jirage masu saukar ungulu sun yi ta shawagi a samaniyar birnin New Delhi, yayin da dubban ’yan sanda da jami’an tsaro suka ringa yin sintiri a kan titunan birnin. An dauki irin wadannan matakan tsaron da ba a taba ganin irinsu ba a yayin da ake ta zaman fargabar cewa watakila masu tsattsauran ra’ayi zasu kai hari a lokacin wannan bukin hutu mafi muhimmanci a kasar Indiya, watau hutun tunawa da ranar da Indiya ta rungumi tsarin mulkinta a shekarar 1950.
Birnin New Delhi ya girgiza da harin kunar bakin wake da aka kai kan majalisar dokoki a watan jiya, harin da Indiya ta dora laifin kai shi a kan kungiyoyi masu cibiya a Pakistan, makwabciyarta.