Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Samun Ruwan famfo a Garin Goma - 2002-01-26


Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce ma’aikatan agaji sun gyara rabin famfunan ruwan sha na garin Goma a Kwango Kinshasa, inda wani dutse yayi tumbudin narkakken dutse da wuta da kuma toka yau fiye da mako guda. Jami’an sun ce ana sa ran maido da sauran hanyoyin samun ruwan sha na garin nan da mako guda.

An sake bude filin jiragen saman Goma a jiya Jumma’a, inda takaitattun jirage, kanana, suka fara sauka da tashi. An rufe wannan filin jirgin sama tun lokacin da dutsen Nyiragongo yayi tumbudin wuta da narkakken dutse.

Jami’ai sun ce nan bada jimawa ba ake sa ran fara amfani da filin jirgin domin samar da kayayyakin agaji ga mazauna garin Goma.

XS
SM
MD
LG