Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Fiye Da 500 Suka Mutu A Nijeriya - 2002-01-28


Akalla mutane 500 ne suka mutu, a sanadiyar wasu manyan fashe-fashe da suka wakana daki-daki jiya, a birnin Lagos, birni mafi girma a Nigeriya. ’Yan-sanda da ma’aikatan agaji sun tsamo gawarwarki daga karamin mashigin ruwa na Oke Afa dake unguwar Isolo mai makwabtaka da wurin da fashewar ta wakana, a arewacin birnin na Lagos, wuri mai ‘yar-tazara daga barikin sojojin Ikeja inda wadannan fashe-fashe suka wakana.

Kamfanin dillancin labaran "Associated Press" ya ambato kwamishinan ‘Yan-sanda na Jihar Lagos, Mike Okiro, yana cewa wasu daga cikin mutanen da suka firgita, sun yi ta fadawa cikin wannnan mashigin ruwa, domin nisantar wurin da fashe-fashen suke wakana.

Shaidun gani da idanu, sun ce, an tsinci karin wasu gawarwakin jama’a a kan titunan gundumar ta Ikeja.

Jami’an sojoji sun ce, fashewar ta wakana ne, lokacin da wata gobara da ta tashi a wata kasuwa dake bakin hanya, ta yadu zuwa wani rumbun ajiye makamai. An shafe sa’oi ana jin karajin fashewar makamai a birnin na Lagos, inda tagogi suka rika fashewa, kundojin wuta, da wani irin bakin hayaki suka rika yin toroko a sararin Subahana.

A daidai lokacin da makaman sojojin suka ci gaba da yin bindiga, ‘Yan-sanda da sojojin Nijeriyar sun killace wasu daga cikin yankunan birnin, sannan suka rika kwashe jama’a dake zaune wuraren. Cikin wani jawabi da ya yi na musanman, gwamnan jihar Lagos, Ahmad Bola Tinubu, ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu, yana mai cewa fashewar makaman, hatsari ne kawai ya wakana, sabanin jita-jita da ake bazawa ta yin juyin mulki.

Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya kai ziyara yau, a wurin da wannan gobara ta tashi, inda yayi alkawalin cewa, za a gudanar ba bincike mai zurfi. Tun bayan kawo karshen mulkin sojoji a Nijeriya cikin shekarar dubu, da dari tara da casa’in da tara (1999) gwamnatin shugaba Obasanjo ta sha fama da rikice-rikicen kabilanci dana addini da suka yi sanadiyar kashe dubban mutane

XS
SM
MD
LG