Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Afghanistan Da Na Amurka Sun Abka Kan 'Yan al-Qa'ida a Asibiti - 2002-01-28


Sojojin kundubalar Amurka da dakarun Afghanistan sun kai farmaki kan wani asibiti dake kudancin birnin Kandahar, inda wasu mayakan al-Qa'ida shidda suka ja daga cikin damarar yaki tun watanni biyu da suka gabata.

Jami’an gwamnatin Afghanistan, na fadin cewa an kashe wadannan mayaka shidda sanadiyyar wannan harin da aka kai cikin daren jiya, bayan sa’oi da akayi ana ta bata-kashi har zuwa ketowar alfijir.

Kamfanin dillancin labarai na "Associated Press" na fadin wasu daga cikin sojojin kundumbalar Amurika, makalan rigunansu na rubuce da wata kalma mai cewa “muna kaunar New York“, garin da akai harin ta’addancin goma sha daya ga watan Satumba da ake zargin Osama bin Laden da makaraban 'yan kungiyar al-Qa'ida da aikatawa.

Labari na fadin mayakan al-Qa'ida sun bude wuta yayin da suka hango sojojin kundubalar Amurka.

XS
SM
MD
LG