Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Hamid Karzai Yana Birnin Washington - 2002-01-28


Shugaban gwamnatin wucin-gadin Afganistan, Hamid Karzai, ya iso nan birnin Washington domin tattaunawa da shugaba Bush. A ganawar da za su yi yau a fadar White House, ana kyautata zaton shugabannin biyu za su mayar da hankali a gameda batun sake ginin Afganistan, kasar da yaki ya yi raga-raga da ita, da kuma batun yakin da ake fafatawa a halin yanzu, da ‘yan-ta’dda na Taleban da kuma kungiyar al-Qa'ida.

Malam Karzai ya ce, batun tsaro a kasarsa, shi ne al’amarin da akafi nuna damuwa kansa. A lokacin wannan ganawa da shugabannin biyu za su yi, ana kuma kyautata zaton, jagoran na Afganistan, zai takalo batun ayyukan soji, sannan ya jaddada bukatar fadada adadin askarawan rundunar kasashen duniya mai gudanar da ayyukan tsaro a halin yanzu a birnin Kabul, da sauran yankunan kasar ta Afganistan.

Da maraicen jiya lahadi ne, Malam Karzai ya iso nan Amurka, domin wata ziyarar aiki ta kwana hudu.

XS
SM
MD
LG