Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sa'udiyya Ta Ce Ita Ma Zata Bukaci Yin Tambayoyi Ma Fursunoni - 2002-01-28


Kasar Sa'udiyya ta ce, za ta gudanar da nata tambayoyin, ga ‘yan kasarta wadanda ake zargin su ‘Yan-ta’adda ne, kuma Amurika take tsare da su a halin yanzu. Ministan harkokin cikin gidan Sa'udiyya, Yerima Nayef, ya shedawa jaridar al-Watan cewa, masarautar ta na tuntubar gwamnatin nan birnin Washington gameda ‘yan kasar Saudiyar da aka kama a Afganistan, ake tsare da su a sansanin sojin ruwan Amurika na Guantanamo Bay, dake kasar Cuba.

Jaridar ta ambato Minista Nayef yana fatar za a samu hadin kai a tsakanin hukumomin Saudiya dana nan Amurika gameda wadannan fursunoni da aka garkame. Ya ce, muddin aka damka masu fursunonin, hukumomin Saudiya za su yi masu tambayoyi, sannan su hukunta su, bisa sakamakon bincike ko kuma ganawar ta su.

Amma jami’an bangarorin biyu ba su ce uffan ba, a gameda, adadin ‘yan kasar ta Saudiya dake cikin fursunonin yaki na kungiyar al-Qaeda da Taleban su 158, da ake tsare da su a sansanin na Guantanamo.

XS
SM
MD
LG