Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin Kungiyar Tarayyar Turai Suna Tattauna Batun Sanyawa Zimbabwe Takunkumi - 2002-01-28


Ministgocin Kungiyar Tarayyar Turai dake ganawa a Brussels suna tattauna yiwuwar kakabawa kasar Zimbabwe takunkumi. Sakataren harkokin wajen Britaniya, Jack Straw, shi ya tado da wannan batu a wurin fara taron na yau litinin. Gobe talata za a kammala wannan taro. Britaniya tana son a sanyawa Zimbabwe takunkumi idan shugaba Robert Mugabe ya ki yarda ya kyale 'yan kallon kasashen waje su sa idanu kan yadda za a gudanar da zaben shugaban kasa a watan Maris.

Matakan takunkumin da ake nazarin yiwuwar dauka sun hada har da garkame dukiyoyin shugaban tare da haramta masa tare da mukarrabansa yin tafiye-tafiye a kasashen waje.

Amma kuma, ma'aikatan jakadanci sun ce tana da wuya Kungiyar Tarayyar Turai ta sanyawa Zimbabwe takunkumi a cikin sauri.

Wani kakakin firayim minista Tony Blair na Britaniya, ya ce har yanzu Mr. Mugabe yana da damar kaucewa fuskantar takunkumi ta hanyar kyale 'yan kallo da 'yan jaridan kasashen waje su sa idanu kan yadda za a gudanar da zaben watan Maris. Ya kuma ce Britaniya tana son jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar ta kawo karshen kai hare-hare kan 'yan adawa.

Daga can cikin Zimbabwe, gidan rediyon kasar ya ce Shugaba Mugabe ya gayyaci 'yan kallon kasashen waje su sanya idanu kan zaben, amma ban da 'yan kallo daga Britaniya. Mr. Mugabe ya ce Kungiyar Commonwealth da Kungiyar Tarayyar Turai da sauran kungiyoyi zasu iya tura 'yan kallonsu, amma ban da Britaniya wadda yayi zargin cewa tana daurewa 'yan adawa gindi.

XS
SM
MD
LG