Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'ikatan Agaji Sun Zakulo Daruruwan Gawarwaki a Nijeriya - 2002-01-28


Ma’aikatan agaji a Najeriya sun ce sun zakulo daruruwan gawarwaki da gini ya rufta dasu bayan tashin da wasu bama bamai sukayi a can Lagos. Shaidun gani da ido na fadin akalla mutum dari biyar sun halaka, mafi yawansu duk yara, yayin da suke kokarin tsira daga fashewar wadannan nakiyoyi ta hanyar daka tsalle suna fadawa ruwa a gundumar Ikeja.

Koda yake hukuma bata fadi adadin mutanen da suka halaka sanadiyar fashewar wadannan bamai bamai ba, labari na fadin cewa ana ganin gawarwakin kwance a kan tituna.

Tuni a yau shugaba Obasanjo ya kai ziyara inda wannan ala’mari ya afku, kuma yayi alkawarin za’ayi cikakken bincike, hakazalika yayi alkawarin za’a tallafawa wadanda suka rasa gidajensu. Jami’an gwamanati na fadin cewa wadannan bama bamai sun fara tashi ne, a daren jiya lahadi, bayan wata wuta ta kama a rumbun ajiye makamai, dake sansanin sojin Najeriya na Ikeja, inda akace an walcakalar ba’a kulawa da shi kamar yadda ya kamata, ya haddasa tashin wadanna nakiyoyi da suka hada da makaman dake jibge a wannan rumbun makaman.

Jim kadan hayaki ya turnike birnin Lagos bayan tagogin dake kusa da wannan wuri duk sun farfashe sanadiyar fashewar bama bamai da suke kunshe a wannan wuri. Dubban mutane sun bar gidajensu, yayin da ba’a san inda wadansu suka shiga ba.

Kwamandan rudunar sojojin dake Ikeja, Birgediya-janar George Emdin, ya nemi gafara sanadiyyar tashin wadannan bamai bamai da suka kawo firgita da tsoro ga al’ummar wannan wuri. Yayin da gwamna Tinubu na jihar Lagos, yayi kira na musamman ta kafofin watsa labaru ga mutane da su kwantar da hankalinsu, abinda ya afku tsautsayi ne ba wai yunkurin hambare gwamnati ba.

XS
SM
MD
LG