Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sama Ya Bace Dauke Da Mutane 92 - 2002-01-28


Ba’a da tabbas game da makomar jirgin saman nan na fasinja na kasar Ecuador, wanda ya bace yau litinin da safe.

Jami’an kamfanin safarar jiragen saman "TAME" na kasar Ecuador sun shaidawa kamfanin dillancin labaran “ASSOCIATED PRESS“ cewa jirgin saman na dauke da fasinjoji 92, kuma ya fadi a kusa da birnin Ipiales dake kan iyakar Colombia, a kololuwar tsaunukan Andes.

Kamfanin dillancin labaran "REUTERS" ya ambaci jami’an kamfanin jiragen saman su na cewa wani hatsari ya faru a kusa da Ipiales. Haka nan kuma kamfanin dillancin labaran ya bada rahoton cewa ma’aikatun kula da jiragen saman fasinjoji na kasar Ecuador da Colombia dukkansu sun ce jirgin saman bata ya yi.

Ba’a da wani labari game da irin halin da fasinjojin jirgin saman da ma’aikatan shi su ke ciki.

A yau litinin da safe,jirgin saman samfurin Boeing 727 ya tashi daga Quito, za shi birnin Tulcan dake kasar Ecuador, mai kimanin tazarar kilomita 10 kudu maso yamma da birnin Ipiales.

XS
SM
MD
LG