Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Zimbabwe, Turai ta ce sai anyi da ita - 2002-01-29


KTTurai ta yi barazanar sanyawa Zimbabwe takunkumin karya mata tattalin arziki da zai maida hankali akan kassara gwamnatin Robert Mugabe -- muddin dai kasar taki amincewa jami’an Turai su zuba ido akan zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Maris. Ministocin Harkokin Waje na TTurai da suka gana jiya a birnin Brussels sunyi kira ga Zimbabwe da ta kyale a kai mata jami’an da zasu kula da zaben da za’a gudanar kan nan da ran uku ga watan Gobe. Sakataren Harkokin Wajen Britaniya Jack Straw wanda yafi kowa zakewa wajen ganin an sanya takunkumin, ya gargadi Shugaba Mugabe da ya bada hadin kansa ga bukatun na Turai ko ya dandana kudarsa. Ya ce tilas Robert Mugabe ya janye ‘yan bangansa ya kuma kyale manema labarai su gudanarda aiyukansu babu tsangwama tareda su kuma mutan kasar a basu sukunin kada kuri’a cikin sa’ida. Cikin abinda ake neman gabatarwa a takunkumin harda rike kudaden ajiyan Mugabe tareda hana masa tafiye tafiye zuwa kasashen waje tareda manyan mukarraban gwamnatinsa su ashirin.

XS
SM
MD
LG