Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Birnin Lagos Sun Fusata - 2002-01-29


Wadannan fashe-fashe da suka abku ranar lahadi da maraice a Lagos, sun yi sanadin mutuwar mutane fiye da 600. Wakilin Muryar Amurka a yankin Afirka ta Yamma, Luis Ramirez, ya ce jama'a suna ta neman jin dalilin da ya sa rundunar sojojin ta tara nakiyoyi masu dan karen yawa a nan cikin gundumar Ikeja, inda ake da cunkoson jama'a sosai.

Shaidu na gani da idanu sun ce gobarar da ta tashi a wata kasuwar gefen hanya dake kusa da nan ita ce ta yadu zuwa rumbun makaman cikin sauri ta kuma haddasa fashe-fashen. Irin fashe-fashen da suka biyo baya kuwa sun cilla karafa da tarkace masu ci da wuta a kan gidaje da kantuna da kamfanonin dake daura da wannan rumbun. Jama'a da suka firgita sun yi ta rantawa da gudu suna neman tudun-mun-tsira.

Jama'a sun dada fusata a bayan hotunan da suka gani a cikin telebijin da jaridu na ma'aikata suna ciro daruruwan gawarwaki daga mashigin ruwan Oke-Afa. Gawarwakin na mutane ne, da yawa daga cikinsu yara, wadanda suka fada cikin wannan ruwa a firgice, amma kuma ruwan ya cinye su a lokacin da suke kokarin yin iyo su tsere ma fashe-fashen nakiyoyin. Shaidu sun ce an danne mutane masu yawan gaske, wasu kuma aka ingiza su cikin ruwan ba tare da son ransu ba a lokacin da daruruwan mutane suka sheko suka doshi wannan ruwa.

A ranar litinin, shugaba Obasanjo ya ziyarci inda wannan hadari ya faru, ya kuma yi alkawarin cewa rundunar soja zata gudanar da bincike sosai. Ya ce gwamnati zata taimakawa dubban mutanen da suka rasa gidajensu.

A cikin jawabin da yayi daga bisani a telebijin da rediyo, shugaba Obasanjo ya ce akalla mutane dari-shida sun mutu a sanadin fashe-fashen na ranar lahadi. Ya bayyana wannan lamari a zaman bala'in da ya shafi kasa baki daya, yana mai kira ga 'yan Nijeriya da su shafe tsawon talata suna yin addu'o'i.

'Yan sanda ba su bayyanan adadin mutanen da suka mutu ba. Kafofin labaran Nijeriya suna kiyasin cewa mutane tsakanin dari-shida da dubu-biyu ne suka mutu. Hukumomi a Lagos idan ba adadi na zahiri aka samu ba, kiyasin dubu-biyu da wasu keyi shakulatin bangaro ne kawai.

Wakilan kungiyar agaji ta Red Cross sun fada a ranar Talata cewa har yanzu ba a san inda wasu dubban mutane suke ba. Kungiyar tana kokarin sada yara su akalla dari-uku da iyayensu. Yaran sun rabu da iyayensu a cikin ribibin jama'a, a lokacin da kowa ya firgita ya fara shekawa da gudu.

Jami'an soja sun ce tun a can baya an bayyana damuwa a kan yadda ake tara nakiyoyi da makamai cikin wannan rumbun dake barikin sojojin Ikeja. A yanzu dai, jami'ai suna kiran jama'a da su guji yada jita-jita kan ko wanene ke da laifi ko alhakin wannan bala'i har sai an kammala bincike tukuna.

XS
SM
MD
LG