Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Lagos Suna Fusace, Yayin da Paparoma John Paul Yake Taya Al'ummar Nijeriya Jaje - 2002-01-29


Mazauna Lagos, birni mafi girma a Najeriya, sun hasala da gwamnatin kasar a bayan bindigar bama-bamai da albarusai a shekaranjiya lahadi da yamma a wani rumbun ajiye makamai, al’amarin da ya haddasa mutuwar mutane fiye da 600.

'Yan Najeriya suna son sanin ko don mi aka jibge bama-bamai da nakiyoyi da albarusai masu saurin bindiga a unguwar Ikeja mai tsatsube da mutane.

A jiya litinin shugaba Olusegun Obasanjo ya yi rangadi a wurin da bama-bamai da nakiyoyi da kuma albarusan suka farfashe sannan ya yi alkawarin cewa za’a gudanar da cikakken bincike akan al’amarin. Kwamandan rundunar sojojin Ikeja, Birgediya Janar George Emdin, ya roki gafara saboda fashe-fashen da kuma saboda irin yadda suka gigita jama’a.

Shugaban kasar ya aiyana yau talata ranar makoki da juyayin wadanda suka halaka a cikin munanan fashe-fashen. Hukukomin Najeriya sun ce wadanda suka rasa rayukansu, sun wuce 600. Yawancin wadanda suka halaka mata ne da yara, wadanda suka nitse a cikin ruwa lokacin da su ke kokarin cetar rai su gujewa fashe-fashen.

A shekaran-jiya lahadi fashe-fashen suka wakana lokacin da wata gobara ta bazu ta game rumbun na ajiye makamai da albarusai wanda ba a kulawa da shi kamar yadda ya kamata.

Makamaida albarusan sun dad suna yin bindiga, al’amarin da ya girgiza tagogin gidajen dake unguwar da kewaye, sannan kuma curin wuta suka yi ta tashi sama. Dubban mutane sun yi asarar gidajensu.

A halin yanzu kuma Paparoma John Paul,ko Pape Jean Paul,ya baiyana alhinin shi ga abun da ya samu al’ummar Najeriya bayan munanan fashe-fashen da suka wakana a rumbun ajiye makamai da albarusai dake birnin Lagos.

Paparoman ya ce cikin bakinciki mai tarin yawa ya samu labarin gagarumar asarar rayukan da aka yi a birnin Lagos sannan ya ce ya na yin addu’oi ga mamatan da ma’aikatan ceto da kuma sauran mutanen dake taimakawa waɗanda su ka auna arziki su ka tsira da rai.

Paparoman ya mika wannan sakon ne cikin wata sanarwar da Cardinal Angelo Sodano, sakataren harakokin wajen fadar shi ta Vatican ya bada.

XS
SM
MD
LG