Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarima Abdullahi Ya Soki Manufar Amurka a Gabas Ta Tsakiya - 2002-01-29


Fadar White House ta shugaban kasar Amurka ta yarda da cewa akwai sabanin ra’ayi tsakanin gwamnatin Amurkar da gwamnatin kasar Sa'udiyya game da matakin sulhun yankin Gabas ta Tsakiya, amma fadar ta ce manufar Amurka game da batun ba za ta sauya ba.

An tambayi wani kakakin fadar ta White House game da batun bayan da Yarima Abdullah mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya ya baiyana cewa babu wanda zai iya kare matsayin gwamnatin Amurka cikin fadan da Isra'ila ta ke yi da Palasdinawa.

Yarima Abdullah mai jiran gado ya fada a cikin wasu hirarraki da yayi da jaridun New York Times da kuma Washington Post cewa manufar Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya ta son rai ce da nunawa Israila fifiko.

Kakakin fadar White House, Ari Fleischer, ya ce akwai wasu abubuwan da Amurka da sauran kasashen duniya suka samu daidaiton baki akai, haka kuma akwai wadanda suka samu sabanin ra’ayi a kan su. Ya ce samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da makwabtanta Larabawa, batu ne wanda ake samun sabani akai.

XS
SM
MD
LG