Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Yayi Kiran A Dage Kangin Da Aka Yi Wa Arafat - 2002-01-29


Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya yi kira da a kawo karshen saniyar-waren da ake mayar da shugaban Palasdinawa, Malam Yasser Arafat. Mr. Annan ya shaidawa manema labarai a birnin Vienna cewa, abu ne mawuyaci Malam Arafat ya iya yin jagoranci, saboda yanzu ba a yi da shi, kuma kusan an yi masa daurin talala a gida.

Tun cikin watan Disambar bara ne, dakarun Isra'ila suka hana Malam Arafat barin helkwatarsa dake birnin Rammallah, yankin yammacin kogin Jordan. Mr. Annan ya kara da cewa, ga shi kuma gwamnatin Bush tana ci gaba da yin korafi gameda yadda jagoran Palasdinawan yake tafiyar da ayyukansa, tana mai matsa masa-lamba da ya dauki kwararan matakan kawo karshen ta’addancin da ake yi wa Isra'ila. Babban sakataren majalisar dinkin duniyar, ya yi nunin cewa, idan aka dakushe tasirin shugaba, shakka babu, za a samu matsaloli.

A halin da ake ciki kuma, wasu sojojin Isra'ila masu jiran ko ta kwana su fiye da hamsin, sun sanya hannu kan wata takarda mai baiyyana aniyarsu ta daina yin aiki a yankin yammacin Kogin Jordan da zirin Gaza.

Sojojin sun ce, kodayake a shirye suke su kare kasarsu, amma ba za su taka abinda takardar kukar tasu ta bayyana a zaman rawa wajen gallazawa da kuma mamaye Palasdinawa ba. An buga wannan korafi ne, a cikin jaridun Isra'ila daban-daban.

Hafsan-hafsoshin Isra'ila ya yi tur da wannan kuka da aka gabatar, yana mai cewa, ba za ta yiwu ba, irin wadannan askarawa na jiran kota-kwana, su yanke shawara gameda irin ayyukan da za su yi, da wadanda ba za su yi ba. Tuni dai, kasashen duniya daban-daban suke caccakar Isra'ila, saboda zargin da ake yi mata na yin amfani da karfi fiye da kima, wajen murkushe boren da Palasdinawa sukan yi.

XS
SM
MD
LG