Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martanin Jam'iyyar Democrat Ga Jawabin Shugaba Bush - 2002-01-30


Yan majalisar dokokin Amurka daga Jam’iyyar Democrat sun bayyana cewar zasu cigaba da nuna goyon baya ga shugaba Bush, a yakin da yake yi da ta’addanci, a kuma lokaci guda suyi aiki tare da shi wajen fuskantar matsalar tattalin arzikin Amurka.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan Amurka, Richard Gephardt, shi ya gabatar da martanin Jamiyyar Democrat ga jawabin da shugaba Bush yayi ga al'ummar Amurka a daren jiya.

Mr. Gephardt yace "...duk da cewa jam'iyyu biyu muke da su a majalisa, amma muna magana ne da murya daya." Bugu da kari, Mr. Gephardt ya ja kunnen abokan gaban Amurka, da cewa ba abinda zasuyi na ban tsoro da zai raba jam'iyyun kasar guda biyu. Sannan ya kara da cewa..

GEPHARDT: "...There were two parties tonight in the House Chamber, but one resolve. Like generations that came before us..."

FASSARA: A yau, jam'iyyu biyu muke da su cikin zauren majalisar dokoki, amma kuma kudurinmu guda ne.Kamar yadda magabatanmu suka yi, zamuyi duk irin namijin kokarin da zamu iya yi muga munyi nasarar yakin karni na 21.

Amma kuma ya fito fili karara, ya bayyana cewa nuna goyon baya ga yakar ta’addancin, ba wai yana nufin duk sun yarda kan hanyoyin warware matsalolin tattalin arzikin kasar ke nan ba. Mr. Gephardt yayi kira da su hada kai tare da girmama juna don shawo kan inda ra’ayoyinsu ya bambanta da juna.

XS
SM
MD
LG