Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba a San Inda Daruruwan Mutane Suke a Lagos Ba - 2002-01-30


Kungiyar agaji ta Red Cross ta Nigeria tace har yanzu akwai daruruwan mutanen da ba’a san inda suke ba a sakamakon gobarar da ta ratsa sansanin adana makamai dake Lagos a ranar lahadi data shige.

Wani mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross, Mr. Patrick Bawa, ya fadawa Muryar Amirka cewa yawancin wadanda suka bacen yara ne ’yan tsakanin shekaru hudu zuwa goma sha daya. Yanzu haka kungiyar Red Cros ta kafa sansanoni guda biyu domin yin rajistar wadanda suka rasa matsuguninsu domin basu kayayyakin abinci da ruwa da kuma mafaka a birnin.

Mr. Bawa yace gano iyaye da ’yan'uwan yaran na ci gaba da zama babbar kalubala.

BAWA:"Some of them are very little children..."

FASSARA: Wasu daga cikinsu, yara ne kanana sosai, a saboda haka ba zasu iya gaya mana irin abubuwan da muke bukatar sani ba. Yawancinsu sunayensu kawai suke iya gaya mana. Baya ga haka basu san komai ba. Sa’annan kuma wasu daga cikinsu suna cikin halin firgita. Muna da wadanda ke samun wahala wajen ji a saboda tashe tashen bama baman. Wadanda suke da wannan matsala an kai su babban asibitin birnin domin ayi musu jinya.

A halin da ake ciki gwamnatin Nijeriya da jami’an sojan kasar sun kaddamar da bincike domin tantance musabbabin fashe-fashen na ranar lahadin data shige. Shugaban Nijeriya, Olushegun Obasanjo, yayi alkawarin cewa za’a yi bincike sosai. Yanzu dai gwamnati tace fiye da mutum dari shidda ne suka mutu.

XS
SM
MD
LG