Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Philippines Da Na Amurka Sun Fara Atusayen Hadin Guiwa - 2002-01-31


Sojojin Philippines dana Amurka sun kaddamar da rawar-dajin hadin guiwa da nufin dakile Musulmi masu zazzafan ra’ayi wadanda aka ce suna da alaka da kungiyar al-Qa'ida a kudancin Philippines.

Hafsan sojojin Philippines, Janaral Diomedio Villanueva, shine ya ayyana fara wannan atusayen yaki da ta’addanci a wajen wani biki da aka yi yau alhamis karkashin tsauraran matakan tsaro a birnin Zamboanga dake kudancin kasar.

Philippines ta jaddada cewa sojojin Amurka dari shidda dake wannan atusayen, zasu fi maida hankali wajen horar da sojojin Philippines amma ba zasu yi yaki kai tsaye da kungiyar ’yan tawayen Abu Sayyaf ba. Tuni dama kungiyar Abu Sayyaf ta kashe wani ba'Amerike kuma tana garkuwa da wasu Amerikawa biyu da kuma wata nas ’yar Philippines.

XS
SM
MD
LG