An sami rahotannin dake cewa ana ci gaba da gumurzun yaki tsakanin mayakan sa kan dake gaba da juna a lardin Paktia na gabashin kasar Afghanistan. Rahotannin na cewa jiragen saman yakin Amirka suna shawagi a zagayen inda ake fadan tun safiyar yau Alhamis, amma basu tsoma hannu a rikicin da ake yi ba.
Ana tafka yakin ne domin mallakar Gardez, babban birnin Lardin. Anji aman boma-bomai da bindigogi masu aman harsasai na tashi a yankin. Jami‘an hukumomin yankin sun bayyana cewa mafi yawan farar hular dake zaune a yankin sun tsere tun jiya laraba.
Ance mutane masu dimbin yawa sun rasa rayukansu.