Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi Na Daukar Barazanar Kashe Ba'Amurke Dan Jarida da Karfin Gaske - 2002-01-31


Jami‘an Gwamnatin Amirka da na kasar Pakistan sun bayyana cewa ana daukar barazanar kisan da ’yan ta‘adda suka yi na dan jaridar nan ba‘amurke mai suna Daniel Pearl, da karfin gaske, bayan da suka sace shi a makon da ya gabata a kasar ta Pakistan.

Jami‘an sun ce wata wasikar da ’yan ta‘addar suka aikewa hukuma jiya laraba akwai kanshin gaskiyar aiwatar da barazanar cikinta. Ita kanta wasikar na kunshe da karin wasu hotuna biyu na dan jaridar dake yiwa mujallar cinikayya ta Amurka mai suna "The Wall Street Journal" aiki.

Kungiyar ’yan ta‘addar da suka sace dan jaridar babu wanda ya san ad zamanta a can baya. Sunan kungiyar shine "Kungiyar Masu Kishin Maido da Diyaucin Kasar Pakistan," ta kuma bada sanarwar cewa shi dai dan jarida Pearl dan leken asirin Isra‘ila ne, don haka sun yi barazanar zasu kashe shi saifa idan Amurka ta bada iznin sakin ’yan Pakistan da ta kama a lokacin yakin da take yi da ayyukan ta’addanci a kasar Afghanistan.

Kungiyar ta kuma gargadi dukkan Amerikawan dake zaune a Pakistan da su bar kasar.

XS
SM
MD
LG