Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Ce Ba ta Gamsu da Hujjojin Amurka Ba - 2002-01-31


Kasar China ta nuna rashin amincewarta da zargin da shugaba Bush na Amirka ya yiwa kasashen Iran da Iraq da Koriya ta Arewa a zaman kasashen dake tallafawa ayyukan ta‘addanci da neman kera makamai masu guba.

Mai magana da yawun ma‘aikatar harkokin wajen kasar China ya maida martanin cewa China bata gamsu da hujjar da shugaba Bush ya bayar a jawabinsa na halin da kasa ke ciki ran talata ba, musamman ganin yadda hakan ya sabawa akidar tsarin huldar kasa da kasa. Kakakin na kasar China yana mai cewa abinda China ke son gani shine a kauda son kai a rika baiwa kowace kasa ’yancinta na fada a aji a harkokin kasa da kasa. Yace nuna son kai da ware wasu kasashe a nuna masu kyama zai bata kyakkyawan yanayin dangantakar kasa da kasa, kuma hakan ba zai warware matsalolin da ake fuskanta ba.

Su ma kasashen Koriya ta Arewa da Iran da Iraqi duk sun yi watsi da jawabin na shugaba Bush.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta bada sanarwar cewa shugaba Bush ba shi da niyyar bada umarnin daukar matakin soja a kan kasashen uku da ya ambata.

XS
SM
MD
LG