Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Hamsin a Afghanistan - 2002-01-31


An kashe mutane 50, a sanadiyyar barkewar wani kazamin fada a tsakanin bangarorin dake gaba da juna a yankin gabashin Afganistan, wani lamari dake sa tababa a gameda yiwuwar samun zaman lafiya mai dorewa a wannan kasa da yaki ya dai-daita. A jiya laraba ne, aka kacame bata-kashin a lardin Patkia.

Rahotanni sun ce, wata kungiyar mayaka ‘yan hamayya, wadda ta kwace harkokin iko, bayan da Taleban ta kau, ta wartaki dakarun dake yin biyayya ga sabon gwamnan lardin daga tungarsu ta tsaunukan dake kewaye da birnin Gardez, babban birnin lardin.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambato mayakan dake janyewa, suna cewa, dakarun dake marawa jagoran kabilar Pashtun, Saif Ullah, sun ci karfinsu.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Afganistan, Hamid Karzai, wanda a halin yanzu yake ziyara a London, yau, ya sake jaddada bukatar girke wata gagarumar rundunar tsaro, ta askarawan kasa da kasa, a kasarsa ta Afganistan.

XS
SM
MD
LG