Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon Yana Takaicin Rashin Kashe Arafat - 2002-01-31


Firayim Ministan Isra'ila, Ariel Sharon, ya ce yana takaicin yadda Isra'ila ta ki kawarda jagoran Falasdinawa, Yasser Arafat, a shekarar 1982, lokacin da dakarun Isra'ilar suka yi masa kofar rago a kasar Lebanon.

Mr. Sharon, wanda a lokacin shi ne ministan tsaron Isra'ila, ya shaidawa wata jaridar Isra'ilar cewa, an kulla wata yarjejeniya a Lebanon, kada a kawadda Malam Arafat. Ya ce, amma yana takaicin cimma wannan dawajewa.

Tun dai cikin watan jiya na Disamba ne sojojin Isra'ila suka yiwa Malam Arafat daurin talala a birnin Rammalla, yankin yammacin Kogin Jordan, suna matsa lamba da ya dauki kwararan matakai akan kungiyoyin dake kaiwa Isra'ila farmaki.

Ta daya gefe kuma, dakarun Isreala sun harbe wasu matasa Falasdinawa biyu har lahira, wadanda suka yi wa wani ayarin Isra'ila kwanton bauna a kusa da wata unguwar share ka zaunar Yahudawa dake kudancin zirin Gaza. Mutanen da suka kai harin, sun saki wani bam, sannan suka bude wuta da bindigogi masu sarrafa kansu, a daidai lokacin da wata motar gingimari ta gilma, tana dauke da wasu manoma ‘yan kasar Thailand zuwa wannan unguwa ta share ka zauna.

Mayakan sa kan kungiyar Islama ta Hamas sun dauki alhakin kai yin wannan kwanton-bauna.

XS
SM
MD
LG