Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Neman Yaran Da Suka Bace a Nijeriya - 2002-01-31


Jami’an kungiyar agaji ta Red Cross a Nijeriya suna ci gaba da neman daruruwan yaran da suka bace a bayan fashe-fashen nakiyoyi da makamai a wani barikin sojoji, yayin da jama’a da suka fusata suke bidar bayanin dalilin wannan bala’i.

Kungiyar Red Cross ta ce akwai daruruwan yara a kan tituna a lokacin wadannan fashe-fashe, sannan sun warwatse domin kubutar da rayukansu. Ma’aikata suna tara sunayen wadannan yaran da suka bace a Cibiyar Red Cross da kuma tasoshin ’yan sanda dabam-dabam.

Jaridun Lagos sun ce ’yan sanda suna tsare da yaran da ba a san yawansu ba a ofisoshin ’yan sandan. Wani jami’in Red Cross yayi watsi da rahotannin jaridun, yana fadin cewa ’yan sanda suna basu cikakken hadin kai a kokarin da suke yi na maida wadannan yara ga iyayensu. Ya ce wadannan rahotannin suna kara munin zaman tankiyar da ake yi a tsakanin jama’a.

Mutane sun fusata cikin ’yan kwanakin nan a yayin da suka fara neman bayanin dalilan da suka sanya aka tara nakiyoyi masu dan karen yawa a tsakiyar gundumar da ta fi kowacce yawan jama’a a Ikko. Shugaba Obasanjo yayi alkawarin gudanar da bincike sosai.

An yi imanin cewa fashe-fashen sun kashe mutane fiye da 600, suka sa wasu dubbai suka rasa gidajensu.

XS
SM
MD
LG