Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Sun Kaddamar Da Yakin Neman Zabe a Zimbabwe - 2002-02-04


Babban dan takarar masu adawa a kasar Zimbabwe, yayi kira ga masu jefa kuri’a da su kawar da shugaba Robert Mugabe daga kan karagar mulki a zaben shugaban kasar da za a yi a wata mai zuwa.

Masu goyon bayan Mr. Tsvangirai su dubu goma sha biyu sun hallara jiya lahadi a garin Mutare, tungar ’yan adawa, a yamma da babban birnin kasar inda suka kaddamar da yakin neman zaben Mr. Tsvangirai.

Mr. Tsvangirai ya ce tilas masu jefa kuri’a na kasar Zimbabwe suyi zabi a tsakanin makoma maras haske a karkashin Mr. Mugabe, ko kuma abinda ya kira zaben kwarai na gwamnatin hadin kan kasa karkashin jam’iyyarsa ta ’yan rajin sauyi mai suna MDC.

Mr. Tsivagirai yace ba wani abinda gwamnatin Mugabe ta tsinana cikin shekaru 22 da tayi tana mulki, im ban da koma bayan tattalin arzikin Zimbabwe da kuma tarzomar siyasa da hakan ya zama sanadiyyar dagula rayuwar miliyoyin al’umar kasar.

XS
SM
MD
LG