Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Adawa A Gabashin Afghanistan Zasu Kara Tattaunawa - 2002-02-04


A yau litinin bangarorin da ba su ga maciji da juna a garin Gardez dake gabashin Afghanistan zasu kara tattaunawa da junansu, tare da taimakon wasu jami’an gwamnatin wucin gadin shugaba Hamid Karzai.

A tattaunawar da akayi jiya, bangarorin biyu duk sun yarda su tsagaita bude wuta a tsakaninsu, domin shawo kan takaddamar dake da akwai tsakaninsu, yayin da sama da mutum hamsin suka hallaka a makon jiya a garin na Gardez, babban birnin lardin Paktia, inda akayi wata arangama tsakanin dakarun wani madugun sojojin sa kai da kuma dakaru masu goyon bayan gwamnan wannan lardi wanda ba shi da farin jini.

Shugabannin kabilun wannan lardin na zargin sabon gwamnan, Padshan Khan, da laifin cin hanci da kuma mugunta ga al’ummar wurin, saboda haka suke kira ga shugaba Karzai ya maye gurbinsa da wani.

XS
SM
MD
LG