Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Fadan Kabilanci a Nijeriya - 2002-02-04


Wannan sabon fada na kabilanci ya barke ranar asabar tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ikko, cibiyar kasuwanci ta Nijeriya. Wakilin Muryar Amurka, Luis Ramirez ya ce Hausawa 'yan arewa, sun jima suna tsama da Yarbawan yankin kudu maso yammacin Nijeriya.

Babu tabbas kan abinda ya haddasa barkewar wannan sabuwar fitina a unguwar Idi Araba. Amma shaidu da yawa sun ce fitinar ta faro ne daga wani sabanin da ya shiga tsakanin wani iyalin Hausawa da na Yarbawa. Daya daga cikin iyalan ya zargi dayan da laifin nuna rashin mutunci.

A fadan da ya biyo bayan wannan sabanin ra'ayi, an ce Hausawa da Yarbawan sun yi ta jifar junansu da duwatsu da kwalabe, suka kuma kona gidaje da kantuna da ababen hawa.

An ce kura ta lafa ranar lahadi a unguwar ta Idi Araba, a bayan da 'yan sanda suka shiga suka mamaye unguwar. Amma shaidu sun ce sabon fada ya sake barkewa ranar litinin. Shaidun suka ce jim kadan a bayan da 'yan sanda suka fice daga wannan yanki sai mayakan sassan suka fara kai hari kan junansu da bindigogi da adduna. Ala tilas daruruwan mutane suka gudu suka bar gidajensu.

An sake girka 'yan sanda a yankin. Gwamnan Jihar Lagos, Bola Tinubu, ya ce ya umurci dakarun tsaro da su murkushe wannan tashin hankali ko ta halin kaka, yana mai cewa tura ta kai bango haka.

Wannan tashin hankali na baya-bayan nan, ya zo daidai lokacin da zaman tankiya ya kara yin tsanani a Nijeriya, kasar da ta fi kowace yawan jama'a a Afirka. A ranar asabar Nijeriya ta samu nasarar warware yajin aikin farko na 'yan sandanta, yajin aikin da ya tilastawa bankuna da wasu kamfanoni da kantuna rufe kofofinsu a ranar Jumma'a a fadin kasar.

Ga shi kuma gwamnati tana kokarin magance abubuwan ad suka biyo bayan fashe-fashen da suka wakana a rumbun tara makamai da harsasai da nakiyoyi, inda mutane fiye da dubu daya suka mutu.

A cikin furucin da yayi daren lahadi a gidan telebijin na kasar, Shugaba Olusegun Obasanjo ya ce za a bayyana sakamakon binciken fashe-fashen da zarar an kammala shi.

Wadannan matsaloli na baya-bayan nan suna kara matsin lamba a kan shugaba Obasanjo, wanda ake kyautata zaton zai sake tsayawa takarar neman wannan kujera ta shugabancin Nijeriya a cikin shekara mai zuwa. Shugaba Obasanjo ya hau mulki a shekarar 1999, ya maido da mulkin farar hula a bayan da sojoji suka jima suna jan ragamar kasar.

XS
SM
MD
LG