Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Turai Sun Ce Ba Zasu Sanyawa Zimbabwe Takunkumi Ba - 2002-02-04


Kungiyar Tarayar Turai, KTT, ta yanke shawarar ba zata kakaba takunkumin tattalin arziki kan kasar Zimbabawe a halin da ake ciki yanzu ba, saboda shugaba Mugabe ya kyale ’yan kallon zabe na kasashen kungiyar su halarci zaben kasar da za’ayi a cikin watan Maris mai zuwa. Wata mai magana da yawun KTT, ita ce ta bayyana haka a can Brussels, inda tace ba wani yunkuri daga gwamnatin Zimbawe na hana masu lura da zabe na kasa da kasa kasancewarsu cikin kasar, yayin da zaben shugabancin kasar yake kara kawo jiki.

Mallamar dake magana da yawan kungiyar ta tarayar turai, tayi tsokacin cewa saboda haka ba wata fa’ida a kakaba takunkumin tattalin arziki kan kasar Zimbabwe.

A makon jiya ministocin KTT suka ja kunnen gwamnatin shugaba Mugabe, kan cewa zasu kakaba takunkumin tattalin arziki kan kasar, muddin gwamnatinsa bata kyale ’yan kallon kasashen wajen halartar zaben shugabacin kasar ba.

XS
SM
MD
LG