Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 100 Suka Mutu A Rikicin Kabilanci a Nijeriya - 2002-02-05


Jami‘an ayyukan lafiya a Nijeriya sun ce yawan wadanda suka rasa rayukansu a dalilin rikicin kabilancin birnin Ikko yanzu ya kai dari, a bayan da aka kwashe kwanaki uku ana rikicin.

Har yanzu dai ance sojojin Nijeriya suna zaune cikin shiri. Ko a yau ma an bada rahoton tashin hankalin.

Wadanda suka ganarwa idonsu anji suna cewa an tura soja da ’yan sanda dauke da makamai domin sintirin hadin gwiwa da nufin kokarta kawo karshen rikicin da ake yi tsakanin Hausawa ’yan arewa da Yarabawan kudu maso yammacin kasar.

Kwanaki uku ke nan a jere tun daga daren lahadin da ta gabata kabilun biyu ke tafka fada a tsakaninsu. An yi amfani da adduna, da bindigogi da dai sauran makamai tare da cinnawa gine-ginen jama‘a wuta a lokacin rikicin.

Rikicin ya tilastwa dubban jama‘a yin gudun hijira ala dole. Har yanzu ba’a tantance da abinda ya janyo rikicin ba.

XS
SM
MD
LG