Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aiki Ya Tsayar Da Komai a Antananarivo, Madagascar. - 2002-02-05


Komi ya tsaya cak a babban birnin kasar Madagascar a yau talata, a daidai lokacin da dubban daruruwan mutane su ke yin yajin aikin zama cikin gidajensu domin nuna rashin yardar da sakamakon zaben sahugaban kasar da aka yi a cikin watan Disemban da ya gabata.

Shaidu sun ce akasarin birnin Antananarivo ya dade, babu ko tsuntsu a waje, an dakatar da zirga-zirgar motocin safa, da yake mazauna birnin sun amsa kiran shugaban ’yan adawa Marc Ravalomanana, na maida babban birnin kango.

Ana yin yajin aikin ne na yau bayan an yi makonni ana yin zanga-zangar da ake kyautata zaton za’a ci gaba da yinta a gobe laraba.

Hukumar zaben kasar Madagascar ta yanke cewa tsakanin dan takarar ’yan adawa Mr. Marc Ravalomanana da shugaban kasar na yanzu Didier Ratsiraka, babu wanda ya samu isassun kuri’un da ake bukata domin lashe zaben kai tsaye, a zaben shugaban kasa na watan disemba.

An tsaida cewa za’a yi zabe a zagaye na biyu, domin fitar da gwani, a ranar 24 ga watan na fabarairu, idan Allah Ya gwada mana.

XS
SM
MD
LG