Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Sammacin Tsohon Shugaban Kamfanin ENRON - 2002-02-05


Kwamitocin majalisar dokokin Amurka biyu sun shirya aikewa Kenneth Lay, tsohon shugaban kamfanin makamashin nan na Amurka ENRON, da takardar sammaci, domin ya gurfana gabansu ya bada shaida kan abinda ya janyo rushewar jarin cinikayyar kamfanin.

Kwamitin cinikayya na majalisar dattawan Amurka da kwamitin harkokin kudi na majalisar wakailai duk sun shirya aikewa da takardar sammacin.

Mr. Lay ya janye shirin bada shaidar da yayi niyya tunda farko a jiya litinin. Lauyoyin dake kare Mr. Lay sun bayyana cewar wasu daga cikin ’yan majalisar dattawan suna so ne a shirya tattaunawar ta tsarin tuhuma, wanda hakan bai dace ba, kuma akwai rashin adalci.

A halin da ake ciki, Joseph Berardino, shugaban kamfanin nan na binciken kudi na Arthur Anderson, wanda ke binciken kudaden kamfanin makamashi na ENRON, zai gurfana gaban kwamitin harkokin kudi na majalisar wakilan Amurka domin ya bada shaida.

XS
SM
MD
LG