Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Ci Gaba a Kokarin Gano Dan Jaridar Amurka da Aka Sace - 2002-02-05


Jami‘an ayyukan bincike na Amurka da Pakistan sun ce babu wani ci gaban da aka samu na kirki a neman da suke yiwa dan jaridar Amurkan nan, Daniel Pearl, wanda aka sace a birnin Karachi dake kudancin Pakistan kusan makonni biyun da suka gabata.

Dan jaridar, wanda ke yiwa jaridar harkokin kasuwanci ta "The Wall Street Journal" aiki, ya bace ne bayan da ya shaidawa matarsa cewar zai je domin tattaunawa da shugaban wata kungiyar ’yan jihadin Islama.

'Yan sandan Pakistan sun kama mutane da dama domin yi musu tambayoyi, kuma suna ci gaba da neman karin bayani kan irin rawar da wasu suka taka wajen taimakawa dan jarida Pearl gudanar da ttataunawar kafin bacewarsa.

Gwamnatin shugaba Bush ta yaba da kokarin da gwamnatin Pakistan ke yi. Wadanda suka kame dan jaridar na Amurka sun yi barazanar cewa zasu kashe shi, saifa idan Amurka zata sako fursunonin Pakistan da ta kama a rikicin Afghanistan.

XS
SM
MD
LG