Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaysia Ta Ce Ba Zata Mikawa Amurka Wani Tsohon Soja Ba - 2002-02-05


Gwamnatin kasar Malaysia ta ce ba za ta iza keyar wani tsohon kyaftin zuwa Amurka ba, wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin taka rawa cikin hare-haren da aka kawowa Amurkar a ranar 11 ga watan satumba.

Jami’ai sun ce za’a hukumta Yazid Sufaat wanda aka tsare tun cikin watan Disemba, bisa tsarin dokokin kasar Malaysia. Gwamnatin kasar Malaysia ta zarge shi da zama dan wata kungiyar Musulmin kasar mai neman kafa gwamnati mai bin dokokin Islama sau da kafa.

Amma jami’an binciken Amurka sun ce haka kuma shi dan wata kungiyar Musulmi ce ta kudu maso gabashin nahiyar Asiya, wadda ke da dangantaka da kungiyar al-Qa'ida ta ta’addanci.

Jami’an gwamnatin Amurka sun ce watakila Malam Yazid ya karbi bakuncin wasu mutane ukku masu alaka da hare-haren na ranar 11 ga watan satumba.

XS
SM
MD
LG