Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 22 Suka Mutu a Hadarin Jirgin Kasa a Afirka ta Kudu - 2002-02-06


'Yan sandan Afrika ta Kudu sun ce an kashe akalla mutum ashirin da biyu kuma dari da goma sha bakwai suka ji rauni a hatsarin wani jirgin kasa a lardin Kwazulu Natal dake gabashin kasar.

Yawancin wadanda suka mutu yara ne 'yan makaranta dake cikin wannan jirgin kasan fasinja da ya saba jigila tsakanin Kwadukuza da Durban.

A jiya talata wannan jirgin kasa na fasinja yayi karo da wani jirgin daukan kaya a kusa da Charlottes Dale, kimanin kilomita saba’in a arewa da birnin Durban mai tashar jiragen ruwa.

Har yanzu ba’a tantance musabbabin wannan hatsari ba, kuma za’a kaddamar da bincike.

Hatsarin ya auku ne watanni biyu bayan hatsari makamancin wannan da ya auku a kusa da birnin Durban, inda mutum guda ya mutu, wasu su kusan talatin kuma suka ji rauni.

XS
SM
MD
LG