Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Leken Asiri Ta CIA Ta Ce Har Yanzu Akwai Barazanar Ta'addanci - 2002-02-06


Daraktan hukumar ayyukan leken asiri ta Amurka, C-I-A a takaice, George Tenet, ya ce har yanzu Osama bin Laden da kungiyarsa ta ‘yan-ta’adda ta al-Qa'ida, su na barazana ta kurkusa kuma mafi kamari ga Amurka.

A shaidar da ya bayar a zauren majalisar dokoki a karon farko, tun bayan hare-haren ta’addanci na 11 ga watan Satumba, Mr. Tenet ya shaidawa kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyukan leken asiri cewa, an kama almajiran kungiyar al-Qa'ida kusan dubu daya a kasashe fiye da 60, wani mataki da ya dugunzuma yiwuwar kaddamar da wasu hare-haren na ta’adda.

Sai dai kuma, Mr. Tenet ya yi nunin cewa, har yanzu ba a tarwatsa al-Qa'ida ba, kuma za ta cigaba da kaiwa Amurka farmaki a gida da waje.

Daraktan hukumar ta C-I-A ya ce Amurka da cibiyoyin muradun kawayenta a nahiyar turai, da gabas ta tsakiya, da Afrika da kuma kudancin Asiya, sun fi fuskantar kasadar irin wannan farmaki.

XS
SM
MD
LG