Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijeriya Yayi Kashedin Cewa Tashin Hankali Na Iya Gurgunta Dimokuradiyya - 2002-02-07


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya yayi gargadin cewa akwai babban hatsarin cewa tashin hankali yana iya mamaye kasarsa, ya kuma gurgunta mulkin dimokuradiyya a daidai lokacin da ake shirin yin zabe a shekara mai zuwa.

Mr. Obasanjo yayi wannan kashedin ne jim kadan kafin ya gana yau alhamis a Abuja, babban birnin tarayya, da firayim minista Tony Blair na Britaniya domin tattauna raya kasa da wasu batutuwan.

Mr. Obasanjo ya shaidawa shugabannin siyasa da manyan jami'an tsaro cewa da alamun 'yan Nijeriya suna gangarawa cikin abinda ya kira ukubar tashin hankali, da fitina da rashin bin doka wajen gudanar da harkokinsu na siyasa.

Shugaban na Nijeriya yayi tur da tashe-tashen hankulan kabilanci na tsawon kwanaki hudu da aka yi a Lagos, inda aka kashe mutane 100.

Batun tashin hankali yana buwayar ziyarar firayim minista Tony Blair na Britaniya a Nijeriya, zangonsa na farko a rangadin kasashe hudu da zai yi a yankin Afirka ta yamma. A bayan tattaunawar da yayi da shugaban na Nijeriya, Mr. Blair ya shaidawa 'yan jarida cewa wannan ita ce dama mafi a'ala da ake da ita a wannan lokaci na tabbatar da nasarar kawance tsakanin Afirka da kasashen da suka ci gaba. Ya ce talauci da tashin hankali a nahiyar Afirka, suna iya shafar kasashen yammaci, yana mai nuni da cewar kasashen duniya sun dogara kan junansu ne a wannan zamani.

Mr. Blair, wanda shine firayim ministan Britaniya na farko da ya ziyarci Nijeriya tun 1988, zai yi jawabi gaban zama na musamman na majalisar dokokin tarayyar Nijeriya a yau alhamis. Britaniya ce tayi wa Nijeriya mulkin mallaka.

Sauran wuraren da Mr. Blair zai yada zango sun hada da kasashen Ghana da Saliyo da kuma Senegal.

XS
SM
MD
LG